Kundin Al'ajabi Book 1 by Mansur Usman Sufi

Adventure Stories

Kundin Al'ajabi Book 1 by Mansur Usman Sufi

by Mansur Usman Sufi

0 Views
1 Parts

Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta.
Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!.
Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu.
Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne,
Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi.
Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi,
Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa,
Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi,
Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa.
Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba,
Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske,
Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya,
Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa,
Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi ba.
Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo daga cikin keken dokin,
Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa.
Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya,
Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba.
Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari,
Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da ke gudana ba,
Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya aka sakata a cikin wannan akwatu?
Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan.
An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin akwatin?
Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen,
Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi, adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu.
Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen keken dokin,
Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice.
A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu.
Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar bata raye a halin yanzu.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat? Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne".
Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa sama.
Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin dawakansu suka koma izuwa cikin dajin.
Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar jaririyar?
Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?.

Rate & Review this Book

Please log in or register to submit a review.